Ali Modu Sheriff zai iya gyara PDP?

Image caption PDP ta fada cikin rikici tun bayan zaben shekarar 2015.

Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP, ta nada tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sheriff, a matsayin sabon shugabanta na riko.

Jam'iyyar ta sanar da nada Ali Modu Sheriff ne bayan taron da babban kwamitinta ya gudanar a Abuja.

Ali Modu Sheriff, wanda da shi aka kafa jam'iyyar APC mai mulki, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP gabanin zaben shugaban kasar na shekarar 2015.

A wancan lokacin, ya tsaya takarar dan majalisar dattawa amma marigayi Sanata Ahmed Zanna ya kayar da shi.

Zai iya kawo sauyi a PDP?

PDP dai ta fada rikici ne tun bayan zaben shugaban kasar da aka yi a watan Maris na shekarar 2015, lamarin da ya kai ga saukar shugabanta, Alhaji Ahmed Adamu Mu'azu.

Bayan saukar tasa ne Uche Secondus ya zama shugaban riko, ko da ya ke wasu manyan 'yan jam'iyyar daga arewa maso gabashin kasar, karkashin jagorancin Ahmed Gulak, tsohon mai bai wa tsohon shugaban kasar shawara a kan harkokin siyasa, sun kalubalancin nadin nasa a gaban kotu.

Ahmed Gulak dai ya ce kundin tsarin mulkin jam'iyyar ya bukaci wani daga yankin nasu ya kammala wa'adin Adamu Mu'azu.

Kotu ta amince da bukatar Ahmed Gulak, kuma ta ayyana cewa Mista Secondus ba shi da hurumin zaman shugaban jam'iyyar, lamarin da ya sa Gulak din ya ayyana kansa a matsayin shugaban PDP na riko, ko da ya ke daga bisani wasu 'yan jam'iyyar sun nesanta kansu ga wannan ikirarin da ya yi.

Rahotanni dai na cewa yanzu jam'iyyar ta PDP ta rabu zuwa bangarori da dama.

Baya ga haka, 'yan kasar da dama na ganin PDP ce ta jefa su cikin mummunan halin da suke ciki, musamman saboda rahotanni da ke ci gaba da fitowa, wadanda ke nuna yadda ake zargin wasu manyan 'yan jam'iyyar da sace kudaden kasar.

Don haka ne wasu ke tambaya, shin Ali Modu Sheriff zai iya gyara jam'iyyar?