Cin amanar aure ya zama ruwan dare ne?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Wani shirin Talbijin a Masar ya zama sanadin cece-kuce kan cin amanar aure, bayan wani mutum ya yi ikirarin cewa kashi 30 cikin dari na matan aure a kasar na cin amanar mazajensu.

Hukumar da ke sa ido a kan kafafen yada labarai ta kasar ta haramta yin shirin na tsawon kwana 15.

Hakan ya biyo bayan korafe-korafen da mutane suka yi game da kalaman mutumin da ya fusata su.

To ko ya girman matsalar cin amanar aure ta ke a wasu kasashen duniya?

Bincike kan cin amanar aure

Binciken da aka yi a Burtaniya da Faransa da Amurka sun nuna cewa maza sun fi mata cin amanar aure.

Sakamakon wani bincike da wata kungiya ta yi a Amurka a shekarar 2006 (American General social survey) ya nuna cewa, kusan rabin maza da mata ma'aurata sun amince cewa sun taba cin amanar aurensu.

Yayin da a Burtaniya kuwa babban binciken da aka yi kan mu'amalar mata da maza a shekarar 2000 ya nuna cewa, kashi 15 cikin dari na maza sun kusanci wasu mata a shekarun da suka gabaci ta 2000, amma mata kashi tara ne kawai cikin dari suka ci amanar aurensu.

Wani bincike da wata cibiyar da ke sa ido kan ra'ayin jama'a ta Faransa ta yi a shekarar 2014, ya gano cewa fiye da kashi 55 cikin dari na mazan kasar Italiya da na Faransar sun taba yin mu'amala sau daya da wata matar da ba matar da suke aure ba.

Binciken wanda wani shafin intanet da ke taimaka wa mutane cin amanar aure, Gleeden ya dauki nauyi ya kuma nuna cewa, kashi 34 cikin dari na matan Italiya da kuma matan Faransa kashi 32 cikin dari sun taba kusantar wasu mazajen da ba na aurensu ba.

Sai dai babu alkaluma kan cin amanar aure na wasu bangarorin duniya, kamar misali a Masar inda da wuya mace ta fito fili ta amince ta taba kusantar wani namiji da ba mijinta ba ne.