Ana taimaka wa masu tabin-hankali a Benin

A Jamhuriyar Benin, wata kungiya mai suna Saint Camille da wani mutum, Gregorie Ahingbonon sun zage dantse wajen taimaka wa mutanen da ke da tabin-hankali.

Ahingbonon, dan shekara 65, wani bakanike ne, kuma ya shaida wa BBC cewa akwai dubban mutanen da ke da tabin-hankali, amma babu lokitoci da dama da ke kula da su.

Ya ce, "likotici da ke kula da masu tabin-haknali ba su wuce dozin biyu ba, kuma yawanci an fi danganta tabin-hankalin da jifa, ko aljanu, don haka ne muke wayar da kan jama'a domin mayar da hanakali kan wannan matsala."

Wakiliyar BBC, Leila Adjovi, ta ziyarci wani mai tabin-hankali, Aimi, mai shekara 24, inda dan uwansa ya shaida mata cewa yana dukan mutane shi ya sa aka sanya masa sasari a kafa.

A cewarsa, kulawa da shi na da matukar wahala, domin kuwa ana kashe kudade da dama wajen kula da shi.

Gregorie Ahingbonon ya ce akwai bukatar janyo hankalin mutane kan wannan matsala, ganin cewa ana kai masu fama da wannan matsala a wajen masu maganin gargajiya, maimakon asibitin mahaukata.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti