'Mutane sama da 70,000 sun tsere daga Darfur'

Hakkin mallakar hoto

Majalisar dinkin duniya ta ce mutane fiye da dubu saba'in ne suka tserewa tashin hankali a yankin Darfur na Sudan.

Yawancin wadanda suka tsere fadan da ake yi tsakanin dakarun gwamnatin Sudan da kuma 'yan tawaye , sun nemi mafaka ne a wani sansani da Majalisar dinkin duniya ke gudanarwa da kuma Tarayyar Afirka a arewacin Darfur.

Sai dai, Majalisar dinkin duniyar ta ce ta kasa kaiwa ga dubban fararen hula, wadanda suka rasa matsugunansu a tsakiyar Darfur saboda hukumomin Sudan ba su basu iznin shiga yankunan ba