Za a rufe kamfanin sukari na BUA a Nigeria

Image caption Kayayyakin da ake sayowa daga waje na kara farashi a Najeriya saboda tashin dala

Akwai yiwuwar kamfanin sukari na BUA ya rufe masana'antarsa da ke Nigeria, saboda karancin dalar Amurka da yake sayo kayan aiki daga waje da shi.

Shugaban kamfanin, AbdulSamad Rabiu ya shaida wa BBC cewa karancin dalar ya sa kamfanin zai rufe a watan gobe, saboda baya iya sayo isasshiyar madarar sukarin da yake sarrafawa zuwa sukari da ita.

Inda ya kara da cewa "Kusan wata biyu dalar da muka samu daga babban bankin Najeriya, CBN ita ce $200,000 kawai, kuma muna bukatar $15 miliyan kowane wata idan muna so mu yi cikakken aiki. "

Gwamnatin Najeriyar dai ta ce faduwar farashin mai a kasuwannin duniya ya shafi asusun ajiyar kudadenta na kasashen waje, abin da ya sa ta daina raba dalar ga 'yan kasuwa.