'Yan Kannywood na samun horo a Los Angeles

Hakkin mallakar hoto Hafizu Bello
Image caption Hadiza Gabon da BMB na daga cikin wadanda suka je Amurka domin horo

Wasu daga cikin fitattun taurarin 'yan wasan Kannywood da wasu masu shiryawa da ba da umarni a fina-finan Hausa suna ci gaba da samun horo a Amurka.

'Yan wasan sun ce makarantar koyar dabarun shirya fina-finai da ke cibiyar shirin fim ta LA Studio Center.

Hakkin mallakar hoto Hafizu Bello
Image caption Hafizu Bello ya taba samun kyautar babban mai bayar da umurni a fina-finan Hausa
Hakkin mallakar hoto Hafiz Bello
Image caption Jaruma Hauwa Maina ita ma ta ce akwai bukatar kara gogewa a wajen hada fina-finan Kannywood

Wannan ziyara ta zo ne a lokacin da ake shirin bikin bayar da kyatuttuka na Kannywood Awards a watan Maris, da kuma bikin cika shekaru 25 da soma fina-finan Hausa a Najeriya.

A yayin ziyarar, za su ga yadda ake shirya fim na zamani, za kuma su koyi sababbin dabaru na shirin fim wanda zai taimaka wa fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood.

Hakkin mallakar hoto Hafizu Bello
Image caption Hassan Giggs da Kamal Alkali na murnar halatar wannan taron na karawa juna sani
Hakkin mallakar hoto Hafizu Bello
Image caption Ali Nuhu shi ma ya nuna kwazonsa wajen ganin an zamanantar da harkar fim a arewacin Najeriya