'Yan sandan Nigeria sun gargadi 'yan Biafra

Image caption Hukumomin Najeriya na ci gaba da tsare shugaban gidan radiyon masu fafutukar Biafran, Nnamdi Kanu

Shugaban 'yan sandan Najeriya Solomon Arase ya gargadi 'yan Biafra da su daina daukar makamai ba bisa ka'ida ba.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Alhamis, dauke da sa hannun kakakinta, Olabisi Kolawole, ta gargadi 'yan awaren da su daina daukar makamai ko kuma su fuskanci fushin hukuma.

Rundunar ta yi gargadin ne bayan ta samu labarin wani bayani da aka wallafa da ke cewa 'yan kungiyar su tanadi makamai domin kare kansu.

Su dai 'yan awaren Biafra sun sha yin zanga-zanga domin nuna adawa da abin da suka kira wariyar da ake nuna wa kabilar Igbo, dalilin da ya sa suke neman su balle daga kasar.

Mista Solomon ya shawarci 'yan kungiyar da su bi matakan da suka dace wajen bayyana korafe-korafensu, maimakon tashin hankali.