Ana kirga kuri'u a Uganda

Image caption Ana kirga kuri'un da aka kada a zaben Uganda

Ana kirga kuri'un da aka kada a zaben Shugaban Kasar Uganda wanda masu sa ido na Tarayyar Turai suka soki yadda aka gudanar da shi.

Shugaban masu sa idon Eduard Kukan ya ce abin damuwa ne dangane da dogon jinkirin da aka samu wajen kai takardun zabe zuwa wasu rumfunan zabe.

'Yan sanda sun kuma tsare Jagoran 'yan adawa Kizza Besigye na wani dan takaitaccen lokaci, wani mataki da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta yi allawadai da shi.

Inda ta ce hakan ya janyo ayar tambaya game da yadda Ugandan ta damu wajen ganin ta gudanar da zabe wanda ba bu tsoratarwa a cikinsa.