Tarayyar turai ta daidaita da Birtaniya

David Cameron Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr Cameron ya sha alwashin aiki tukuru dan Birtaniya ta ci gaba da kasancewa a tarayyar turai.

Shugabannin kungiyar Tarayyar Turai sun amince da wasu tsare-tsare da za su taimaka wajen ci gaba da kasancewar Birtaniya a cikin kungiyar.

Shugaban Majalisar zartarwar kungiyar, wato Donald tusk ne ya sanar da yarjejeniyar da aka cimma bayan wani taron da aka kwashi lokaci ana yi a Brussels.

Kuma bayan taron ne Firayim Ministan Birtaniya, David Cameron ya shaida wa manema labarai cewa ya cimma yarjejeniya mai armashi, wadda za ta ba wa Birtaniya kasancewa a cikin kungiyar Tarayyar Turai daga baya-baya, wadda kuma ba za ta tilasta mata yin amfani da kudin Euro ba.

A shekarar 1973 ne aka fara fadada kungiyar kasashe masu arziki ta tarayyar turai, kuma a shekarar 1975 ne Burtaniya ta kada kuri'ar jin ra'ayin jama'a na ko ta kasance cikin kungiyar ko akasin hakan kuma sakamakon ya nuna 'yan kasar sun amince zu zama mambar a tarayyar turai.