Za a sanyawa kayan Zaki haraji a Birtaniya

Masu kiba na fuskantar matsala a kafafun su
Image caption Jami'an lafiya sun ce kiba na sanya mutum ya zama rago.

Wani bincike da aka gudanar a Burtaniya, ya gano cewa idan aka kakabawa kayan kwalam da kwalamashe musamman masu zaki harajin kashi 20 cikin 100, zai taimaka wajen rage masu Kiba cikin shekaru goma masu zuwa.

Cibiyar bincike kan cutar Daji ko Cancer a turance, da cibiyar lafiya ta Birtaniya ne suka gudanar da wannan binciken.

Gwamnatin Birtaniya ta yi na'am da wanna bincike kuma tuni ta fara tattaunawa dan lalubo hanyar da ya kamata a fara aiki da matakin.

Amma kanfanonin da ke saida Lemo sun ce akwai hanyoyi masu yawa da ya kamata abi dan rage yawan zakin da mutane ke sha ba lallai sai an kakaba musu haraji ba.

Hakkin mallakar hoto f
Image caption Sinadarin Cholorine na sanya mutum cikin hadarin kamuwa da cutar Dayabitis.

Ya yin da wasu ke ganin cewa a kalla mutane na bukatar samun kuzari na kashi 12 zuwa 15 cikin dari a jikinsu, wanda kuma hakan na samuwa ne daga Sikarin da suke sha, su kuma jami'an lafiya sun ce bai kamata su sha zaki da ya wuce kashi 5 cikin 100 ba

Kididdiga ta nuna idan har aka kakbawa mutane harajin kashi 20 na kayan zaki da suke sha, to za su karkata ne sauran nau'in kayan kwalam da makulashe da babu sikari a cikinsu wadanda suma su an taimakawa wajan sanya mutane narka kiba.

Binciken da hukumar lafiya da cibiyar bincike kan cutar Sankara na Birtaniya suka gudanar,ya nuna a yanzu haka kusan kashi 30 cikin 100 na al'umar kasar masu kiba ne, idan kuma ba a dauki matakin da ya dace ba nan da shekarar 2025 adadin zai kai kashi 34 cikin 100.

Image caption Bincike ya gano kitse ya na yi wa masu kiba illa ga lafiyar su.

An gano idan aka sanyawa ababen taba ka lashe masu zaki haraji shi ma zai taimaka, dan kuwa idan har adadin da ake hasashe na masu kiba zai kai a shekaru 9 masu zuwa to mutane masu kiba za su zama wata gagarumar matsala a Birtaniya.

A karshe cibiyar lafiya ta birtaniya ta ce kasashen da suka fara daukar matakin kakaba haraji kan lemuka da kayan zaki ba wai rage yawan shan kayan zakin kadai aka yi ba, a'a har ma an samu karuwar kudaden shiga da ake zubawa a bangaren kiwon lafiya dan amfanar jama'a.

Rahoton ya fito ne a daidai lokacin da gwamnatin birtaniya ta fara shirin amfani da dabarun rage Kiba tsakanin al'uma wanda zai fara nan da makwanni masu zuwa da Priministan Birtnaiya David Cameron zai jagoranta.