Ba za mu taba Naira ba — Buhari

Hakkin mallakar hoto State House

Shugaban Muhammadu Buhari na Najeriya ya sake jaddada matsayinsa na kin rage darajar kudin kasar, Naira.

Shugaban ya yi wannan furuci ne a wani jawabi a wata tattaunawa ta Shugabannin Africa a kan kasuwanci da saka jari a Sharm El Sheikh da ke Misira.

Buhari ya kuma kara da cewa Najeriya ba za ta iya gogayya da kasashe masu arzikin masana'antu ba wadanda ke samar da kayyakin bukatunsu kuma ke gasa a tsakaninsu ba.

Sannan ya kara da cewa Najeriya ba ta fitar kayyaki sai dai shigowa da komai da komai har da tsinken sakace don haka bai ga dalilin da zai karya darajar Naira ba.

Sama da masu fada a ji dubu ne ke halartar taron a Misira, ciki har da shugabannin kasashen Africa da Ministoci da kuma 'yan kasuwa.