Dawson ya tsawaita kwantiraginsa da West Brom

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Craig Dawson ya ce hankalinsa ya kwanta kuma zai kara azama wajen murza wa West Brom leda

Dan wasan baya Craig Dawson ya tsawaita kwantiraginsa da shekara daya da kungiyar West Bromwich Albion.

Craig mai shekaru 25 ya buga wasa 97, inda ya ci kwallaye hudu tun bayan da ya koma kungiyar daga Rochdale a watan Augustan 2011.

Kwantiragin dan wasan na yanzu sauran shekara guda ya kare, amma a karkashin kwantiragin da ya sanya wa hannu yanzu zai zauna a kungiyar har shekarar 2018.

"Ina matukar jin dadin taka ledar da nake yi, musamman a cikin shekara daya da rabi da ya wuce domin ina cikin wadanda ake fara wasa da su." Craig ya shaida wa shafin intanet na kungiyar.

Ya kara da cewa "Na kwashe wasu 'yan shekaru a nan kuma iyalina ma sun dawo nan, saboda haka yanke hukuncin tsawaita kwantiragi na abu ne mai sauki."