EU: Cameron zai gana da Ministocinsa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Firayi Ministan Biritaniya David Cameron yayin tattaunawarsu da shugabannin Tarayyar Turai a Brussels

Firayi Ministan Biritaniya David Cameron zai gana da Majalisar Ministocinsa kan makomar Biritaniya a Tarayyar Turai, daga bisani kuma a gudanar da zaben jin ra'ayin jama ar kasar.

Sanarwar gudanar da zaben, zai biyo bayan tattaunawarsa da 'yan majalisar sa ne, a kan sauye-sauyen da ya amince a taron koli na shugabannin Tarayyar Turai da aka yi a Brussels.

Mista Cameron ya ce zai ba da shawarar Biritaniya ta ci gaba da zama a Tarayyar, amma ana jin cewa yawancin Ministocin sa za su goyi bayan kasar da ta fice.

Yarjejeniyar da aka cimma da shugabannin Tarayyar Turai sun hada da ba Biritaniyar damar ci gaba da amfani da kudin kasar Fam, da kuma takaitawa 'yan ci rani daga Turai, wasu abubuwan jin dadi a kasar.