Jiragen yakin Amurka sun kai hari Libya

Hakkin mallakar hoto
Image caption Akasarin wadanda aka kashe a kusa da birnin Sabatha 'yan Tunusia ne.

Jiragen yakin Amurka sun kai hari ta sama a kan kungiyar da ke ikirarin kafa daular Musulunci ta IS, inda akalla aka kashe mutum 30.

An kai harin ne kan wani sansanin horar da 'yan kungiyar, inda ake tsammanin an kashe wani dan kasar Tunisia mai tsastsauran ra'ayi, In ji jami'an Amurka.

Kungiyar ta IS ta kwashe kusan shekara guda tana ayyukanta a Libya, kuma Amurka ta yi kiyasin cewa kungiyar na da mayakan da suka kai 6000 a Libyan.

Kasar ta Libya dai ta kasance cikin rudani tun bayan kifar da gwamnatin marigayi Mu'ammar Gaddafi shekaru hudu da suka wuce.

Akasarin wadanda aka kashe a kusa da birnin Sabatha 'yan Tunusia ne.