Kalubalen da mara lafiya ke fuskanta a Nijar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mata a Jamhuriyar Nijar suna fama da karancin kiwon lafiya.

Al'umomi da dama a Jamhuriya Nijar sun shaida wa BBC cewa suna ci gaba da fuskantar matsaloli na samun ingantaccen kiwon lafiya.

Wakiliyarmu a yankin Damagaram ta tattauna da mazauna yankin, inda suka ce suna kwashe sa'o'i da dama suna tafiya kafin su je inda asibiti yake.

Sai dai a shekarar 2012, gwamnati ta bullo da wani shiri na samar da kiwon lafiya kyauta da nufin saukaka wa mata da kananan yara damar samu a kula da lafiyarsu.

Garin Kegyal yana cikin garuruwan da suka amfana da asibiti, kuma mazauna garin sun shaida wa BBC cewa, a yanzu suna zuwa asibitin da aka gina musu, suna masu cewa "hakan ya sa mun samu sauki wajen samun kiwon lafiya".

Mutanen gari Balbaje ma sun shaida wa BBC cewa suna shan wahala wajen zuwa asibiti saboda rashin kyawun hanyoyi.

Nijar dai na cikin kasashen da Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce sun fi fama da mace-macen mata da kananan yara a duniya.