Kawuna sun rabu a PDP kan shugabanci

Ali Modu Shariff Hakkin mallakar hoto Modu Sheriff Twitter
Image caption Ba wannan ne karon farko jam'iyyar PDP ke samun baraka ba kan shugabanci.

Rikicin shugabanci ya kunno kai a jam'iyyar PDP reshen jihar Borno, kasancewar wani bangare na jam'iyyar bai amince da nadin da aka yi wa Alhaji Ali Mpdu Shariff a matsayin shugaban jam'iyyar ba.

Sabanin ikirarin da shugaban jam'iyyar na jiha, wato Baba Basharu ya yi cewa ba sa tare da sabon shugaban.

Mr Mbirza Gabasa shi ne Mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na jihar Bornon, kuma ya shaidawa BBC ce wa suna tare da Ali Modu Sharif dari bisa dari, kuma matsayin da shugabansu na jiha ya dauka, ya yi shi ne ba tare da tuntubarsu ba.

Ya kara da cewa sun zauna baki daya da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ta PDP gabannin nadin sabon shugaban, inda suka yi na'am da Alhaji Ali Madu Shariff a mtsayin shugaban ta na kasa.

Mr Mbirza ya musanta batun da shugaban jam'iyyar na jihar Borno Baba Basharu ya yi na cewa ba a tuntube su ba aka zartar da hukuncin nadin sabon shugaban.