Cameron ya baiyana zaben raba gardama

Firaministan Birtaniya David Cameron Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Firaministan Birtaniya David Cameron

Firaministan Birtaniya David Cameron ya ce za a gudanar da kuri'ar raba gardama game da makomar kasara a kungiyar tarayyar turai a ranar 23 ga watan Juni.

Bayan taron majalisar ministoci da aka kwashe fiye da sa'oi biyu ana yi, Mr Cameron ya ce majalisar ta bada shawarar ci gaba da zama a cikin kungiyar tarayyar turai.

Yace batun ya hada da yadda Birtaniya za ta hada kai da sauran kasashe wajen tabbatar da tsaro.

Yana mai cewa kasancewa a cikin kungiyar tarayyar turai wadda aka sake yi wa fasali da kwaskwarima za ta amfani Birtaniya ta hanyar kara mata karfin tasiri sabanin ficewa wanda zai iya jefa tattalin arzikin Birtaniya da kuma tsaro cikin hadari