Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Fulani sun koka kan tarbiyar 'ya'yansu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan matan fulani kan yini su na gararanba a titunan birane, dan sayar da Fura da Nono.

A cewar shugabanin kungiyoyin Fulanin tallar na zubar da kimar Fulani a idanun duniya, haka kuma yana jefa rayuwar fulanin cikin halin tsaka-mai-wuya ta fuskar tsaro a saboda haka suka ce maimakon tallace-tallace ya kamata 'yan matan Fulanin su koma makaranta.

Ga dai abinda daya daga cikin shugabannin Fulani a kungiyar Miyetti Allah, a jihar Kaduna Malama Khadija Ardijo ta shaidawa BBC.