Kai Tsaye: Bayanai kan zaben Jamhuriyar Nijar 2016

Latsa nan domin sabunta bayanai

Ranar Lahadin nan ne al'ummar jamhuriyar Nijar suke kada kuri'a domin zaben shugaban kasa da 'yan majalisun dokokin kasar. Sashen Hausa na BBC na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da abin da ke wakana a rumfunan zabe a jamhuriyar ta Nijar da ma wasu jihohi a Najeriya inda 'yan Nijar mazauna Najeriya ke kada tasu kuri'ar. sai ku cigaba da kasancewa da mu.

7:16 Da misalin karfe 7:00 ne dai ya kamata a rufe rumfunan zabe a Niger da Najeriya.

7:15 An fara kidayar kuri'a a mazabar da ke ofishin jakadancin Niger a Kano

7:14 Wata matashiya 'yar Nijar, mazuniya Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya ta tofa albarkacin bakinta kan zaben.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

7:02 Alhaji Abubakar Khalid, shugaban Yan Nijar mazauna Najeriya ya yi tsokaci kan zaben sa'o'i kadan kafin rufe rumfar zabe a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

6:55 Yadda rumfunan zabe suka kasance a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya

6:50 A bisa dokar zaben jamhuriyar Nijar, sai dan takarar shugaban kasa ya samu kaso 50 bisa 100 na ilahirin kuri'ar da aka kada sannan zai lashe zaben. Amma idan ba bu wanda ya samu kaso 50 to dole ne a je zagaye na biyu ne na zaben.

6:44 Mutane 15 ne dai suke takarar kujerar shugabancin kasar, a inda kuma ake da kujerun majalisar dokoki guda 171.

6:33 Mutane miliyan bakwai da rabi ne daga cikin al'ummar kasar miliyan 18, suka yi rijista domin zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki.

6:20 Magoya bayan Hama Amadou dai na ganin cewa kulle dan takarar nasu a kurkuku bita-da-kullin siyasa ne, al'amarin ma da ya janyo zanga-zanga da kone-kone a kasar.

Hakkin mallakar hoto Getty
Hakkin mallakar hoto Getty

6:05 Tun dai watan Nuwambar 2015 Hama Amadou yake a kurkuku bisa zargin safarar jarirai daga Najeriya zuwa kasar ta Niger, batun da ya musanta. Wannan hotonsa ne yana kada kuri'a a shekarar 2011.

Hakkin mallakar hoto Getty

5:54 Sai dai kuma masu adawa da mohamadou Issoufou, wadanda suka hada tsohon firaiminista kasar, Seyni Oumarou da Hama Amadou wadanda suka zamo na biyu da na uku a takarar shugabancin kasar na 2011, suna inkarin kiraye-kirayen masu cewa a sake ba shi damar tazarce.

Hakkin mallakar hoto Getty
Hakkin mallakar hoto AP

5:46 Wasu 'yan kasar ta Niger dai ganin cewa sakamakon irin rawar da shugaban, Mahamadou Issoufou ya taka wajen dakile ta'addanci a kasar, ya kamata ya dore da mulki domin cigaba da yakar ta'addanci.

Hakkin mallakar hoto
Hakkin mallakar hoto

5: 35 Yanzu haka, akwai dakarun Faransa da kuma jirage marasa matuka na Amurka a jamhuriyar ta Niger domin yakar ta'addanci a yankin Afirka ta yamma

Hakkin mallakar hoto AFP

5: 21 Al'amarin ya haddasa rasa rayuka da dama sannan kuma ya yi sanadiyyar daidaita dubban 'yan kasar da suka hada da mata da kananan yara

5:14 Jamhuriyar Niger na daya daga cikin kasashen da ke kewaye da tafkin Chadi wadanda kuma suke fama da mayakan Boko Haram.

Hakkin mallakar hoto

5:02 Rahotannin na cewa rumfunan zabe za su cigaba da kasancewa a bude har karfe 7:00 na yammacin Lahadin.

4:55 Rahotanni dai na cewa an samu isar wasu kayan zabe a makare zuwa mazabu, amma hukumar zaben kasar ta ce ba za a rufe rumfunan zabe ba har sai wadanda ke kan layi sun kada kuri'unsu.

4:51 'Yan jarida ke nan a lokacin da shugaban Niger, Muhammdou Issoufou yake yi musu bayani jim kadan bayan jefa kuri'arsa.

4:42 Dangane da matsalar tsaro da jamhuriyar Niger take fama da ita, ranar 23 ga Mayun 2013, kasar ta fuskanci manyan hare-hare guda biyu daga kungiyoyin da ke ikirarin kishin addinin Islama, a sansanin sojinta da ke Agadez, da kuma shiyyar hakar ma'adanai na kamfanin Arewa da ke arewacin kasar. Akalla mutane 20 ne suka rasa rayukansu a harin kuma yawancinsu sojoji.

4:27 Wasu 'yan Nijer a jihar ta Legas suke tofa albarkacin bakinsu dangane da zaben da ke gudana a jihar da ma na gida Niger.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

4:09 Wakilinmu na jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya, Umar Shehu Elleman ya tattauna da jakadan jamhuriyar Niger a Najeriya dangane da yadda zaben yake gudana.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

3:56 Zaben na Nijar ya jawo hankalin kasashen duniya, inda daruruwan manema labarai da masu sa ido daga sassa daban-daban na duniya suka yi wa kasar tsinke.

3:50 Wakilinmu Ishaq Khalid ya ziyarci kauyen Hamdallaye da ke jihar Tilleberi, a inda ya tarar da dimbin masu Jefa kuri'a, galibi mata na cigaba da jira a layin zabe, cikin zafin rana domin su kada kuri'unsu. Aikin dai na gudana ba bu tangarda.

3:41 Wakilinmu na jihar Kaduna a Najeriya, Nura Ringim ya sake tattaunawa da wasu 'yan Niger, jim kadan bayan kammala kada kuri'arsu.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

3:38 Ranar 16 ga Satumbar 2010, kungiyoyin da ke tayar da kayar baya, kamar su Al-Qaeda da ke Maghreb, suka sace mutum bakwai, biyar daga cikin su 'yan kasar Faransa ne, daga wata cibiyar ma'adanin Uranium na kamfanin ma'adanan Faransar Areva, dake Arlit a arewacin Nijar. A 2013 ne kuma aka saki sauran 'yan Faransar da aka yi garkuwa da su.

Hakkin mallakar hoto Getty

3:27 Kamar sauran kasashen nahiyar Afirka musamman na yamma da hamadar sahara, Niger tana fama da matsalar tsaro.

Hakkin mallakar hoto Getty

3:19 Wasu 'yan Nijer ke nan suke bayyyana ra'ayinsu dangane da damar kada kuri'a a Najeriya da aka ba su, da kuma sauran batutuwan cigaba da suka shafi kasar tasu ta Niger, jim kadan bayan kammala kada kuri'a a mazabar Tudunwada a Kaduna.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

3:12 Sama da masu kada kuri'a 600 ne aka yi wa rijista a mazabar Tudunwada da ke kaduna a arewacin Najeriya kuma da daman su sun kada kuriar su, kawo yanzu, kamar dai yadda wakilinmu na Kaduna Nura Muhammed Ringim ya shaida mana.

2:42 Yanzu haka dai 'yan takara 14 ne suke kalubalantar shugaban na Nijer, Muhammadou Issoufou, a neman kujerar shugabancin kasar.

2:37 Ranar 12 ga Maris 2010, jagoran jam'iyyar adawa, Mahamdou Issoufou ya lashe zaben shugaban Nijar, a karo na biyu da aka yi zaben mulkin dimokradiyya a kasar. Hawa mulkin da Mahamdou Issoufou ya yi a watan Afrilun shekarar ta 2010 ne ya kawo karshen mulkin sojoji tun bayan kwace mulkin da suka yi a ranar 18 ga Fabrairun 2010.

Hakkin mallakar hoto

2:33 'yan Niger a sashun kada kuri'a a Kano cikin yanayin bin doka da oda ba tare da hayaniya ba. hakan nema ya ba wa wani mai sauraron sashen Hausa na BBC, Aminu Bakanoma Sani Mainagge, sha'awa ya kuma dauki hotunan ya aiko mana

Hakkin mallakar hoto Aminu Abdou Bakanoma

Muryoyin wasu masu niyyar jefa kuri'a amma ba su samu sun yi ba sakamakon rashin sunayensu da kuma katunan zabensu da ba a samu ba duk da cewa sun yi rajista. Ga abin da daya daga cikinsu ta shaida wa wakilinmu Ishaq Khalid

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

2:24 Ranar 18 ga Fabrairun 2010 sojoji suka hambarar da gwamnatin Tandja, bayan wani bata-kashi da aka gwabza, a fadar shugaban kasar. An dora wa Tandja alhakin wannan bore nebisa zargin sauya kundin tsarin mulkin kasar da ya yi a shekarar 2009, domin ya samu damar zaman dirshan kan karagar mulki.

Hakkin mallakar hoto Getty

2:08 Muryar Seini Oumarou, daya daga cikin masu takara don kalubalantar shugaba mai ci, Muhammadou Issoufou, dangane da damuwar da ya nuna kan jinkirin da aka samu na fara zabe a kan lokaci. sai dai kuma ya kara jadda ammannarsa ga mulkin dimokradiyya.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

2:00 Ranar 9 ga watan Afrilun 1999, an kashe Ibrahim Mainassara, lokacin juyin mulkin da masu tsaron fadar shugaban kasar suka jagoranta. Daga bisani kuma bayan watanni takwas Mamadou Tandja ya maye gurbi gwamnatin mulkin sojan.

Hakkin mallakar hoto Getty

1:54 Shugaban jamhuriyar Nijar, Mohamadou Issoufou, ya bayyana fatan zaben kasar da ake gudanarwa a yau zai karfafa tsarin dimokradiyya a kasar. Sai dai ya ce hakan ba zai tabbata ba sai 'yan kasar sun gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali da lumana. Shugaban wanda daya ne daga cikin 'yan takarar zaben na yau, ya kara da bukatar 'yan kasar da su kada kuri'arsu ga duk wanda suka ga ya dace ya ciyar da kasar gaba. Shugaban ya bayyana hakan ne ga 'yan jaridu bayan da ya kada kuri'arsa. Wakilinmu Ishak Khalid ya nado muryarsa.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

1:46 Ranar 27 ga Janairun 1996, Ibrahim Bare Mainassara ya jagoranci juyin mulkin da ya hambarar da Mahamane Ousmane, shugaba na farko da kasar ta zaba na mulkin dimokradiyya a wannan lokacin.

1:28 Ranar 15 ga watan Afrilun 1974, ne babban hafsan sojin kasar, Seyni Kountche ya jagoranci juyin mulkin da ya hambarar da shugaba Diori Hamani. Koutche ya gudanar da mulkin mallaka har lokacin mutuwarsa a shekarar 1987.

Hakkin mallakar hoto Getty

1:18 Jamhuriyar ta Niger ta koma turbar mulkin dimokradiyya a shekarar 1990, bayan kwashe tsawon lokaci tana fama da mulkin soja.

Hakkin mallakar hoto Getty

1:13 Kiyasi ya nuna cewa al'ummar kasar Nijar sun kai miliyan 18.

Hakkin mallakar hoto Getty

1:05 Wasu masu Jefa kuri'a a Yamai sun koka saboda ba su ga sunayensu ba, kuma ba a samu katinnansu ba duk da cewa sun yi rajista.

12:57 Wasu 'yan Niger a Kano da suka je zabe ba tare da katin zabe ba, an umarce su cewa su tsaya sai 4:00 na yamma za a basu dama su yi zabe, in dai da sunansu a cikin rijista.

12:47 Wakilinmu da ke a Yamai yanzu haka, Ishaq Khalid ya ce duk da cewa Seyni Oumarou ya nuna damuwa kan jinkirin bude wasu rumfunan zabe, amma yana da kwarin gwiwar za a kammala zaben salin alin.

12: 45 Elhadji Seini Oumarou, ke nan, na jma'iyyar MNSD Nasara, daya daga cikin 'yan takarar adawa yake kada tasa kuri'ar da misalin 11:40, a mazabar Ecole Kano Koiira kano est da ke Niamey. Ya kada kuri'ar tare da matarsa, Aissa.

12: 41 Sai dai kuma duk da arzikin da Allah ya huwace wa kasar, Niger ta yi kaurin suna a duniya ta fannin fama da talauci da yunwa.

12:39 Nijar dai Kasa ce mai rairayin hamada, da ke da albarkatun ma'adanan Uranium da zinari da karfe da kuma man fetur.

Hakkin mallakar hoto Getty

12:31 Wakilinmu na Kano, Yusuf Ibrahim Yakasai ya ce ana gudanar da zaben a Kano cikin tsattsauran matakan tsaro, inda ake tantance duk wani da ke son shiga ofishin jakadancin domin kada kuri'a. Komai dai na gudana ba tare da wata matsala ba.

12:20 'Yan jamhuriyar Niger masu zabe, a kan layi suna jiran su kada kuri'a a mazabar ofishin jakadancin Nijer a Kano.

12:17 A jihar Kano da ke arewacin Nigeria kuwa da misalin karfe takwas na safe ne aka fara kada kuri'a, a karamin ofishin jakadancin Niger da ke jihar. Akwatuna biyu ne dai ake jefa kuriun a ciki a kanon. Karamar jakadar Nigeria Hajiya Rabi Dodo ta shaida wa wakilinmu na Kano, Yusuf Ibrahim Yakasai cewa sama da mutane 451 ne suka karbi katinsu na zabe daga cikin mutane 708 da suka yi rijista. Sai dai tace duk wanda sunan sa ya fito a rijistar zai yi zabe ko da bai karbi kati ba.

12:13 Masu sa ido kan sha'anin zabe a Nijar sun ce kawo yanzu, a jahar Damagaram komai na tafiya dai-dai, duk da cewa an samu korafe-korafe daga jam'iyyun siyasa kafin daga bisani su samu yadda suke so, kamar dai yadda Sadat Illiya Dan Mallam ya shaidawa wakiliyarmu Tchima Illa Issoufou.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

11: 59 Jamhuriyar Niger dai ta samu 'yancin kai daga mulkin turawan mallaka na kasar Faransa, a ranar 3 ga Agustan 1960.

Hakkin mallakar hoto Getty

11:54 Wasu 'yan Nijer mazauna jihar Lagos suna korafi kan cewa ba a kai musu akwatinan zabe ba a mazabar da suka yi rijista, kamar dai yadda za ku ji a hirar da wakilinmu na Lagos din Umar Shehu Elleman ya tattauna da wasun su kan korafin nasu.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

11:34 Ga kuma yadda tattaunawar da Tchima ta yi da Maryamu wadda ita ma ake zargin ba ta kai shekarun wakiltar jam'iyya ba, a rumfar zabe

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

11:26 Wakiliyarmu ta birnin Damagaram, Tchima Illa Issoufou ta tattauna da wakilan jam'iyyu guda biyu da ake zargin kananan yara ne. Ga yadda tattaunawar ta kasance da Abdurrahman mai shekara 16.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

11:13 Ana dai gudanar da zaben ne a jamhuriyar ta Niger, yayin da daya daga cikin 'yan takarar shugabancin masu adawa watau Hama Amadou ke tsare a gidan yari, bisa zargin safarar jarirai daga Nijeriya. Yana dai musanta zargin, kana magoya bayansa na cewa tsare shi na da nasaba da siyasa.

Hakkin mallakar hoto Getty

11:08 Dokar zaben na shugaban jamhuriyar Niger, ita ce idan dai ba a samu dan takarar da ya samu fiye da kaso 50 cikin dari na illahirin kuri'u da aka kada ba, to wajibi ne a gudanar da zabe zagaye na biyu tsakanin 'yantakara biyu da suka fi samun kuri'u.

10:51 Wakilinmu na Lagos, Umar Shehu Elleman, wanda a yanzu haka yake a mazabar da al'ummar Nijer mazauna jihar ta Lagos suke kada kuri'a ya ce zabe na gudana lami lafiya.

10:48 Ana gudanar da wannan zaben dai a wasu jihohi a Najeriya, a inda 'yan jamhuriyar ta Nijer suke da yawa, kamar jihar Kano da Kaduna da ke arewacin kasar da ma jihar Lagos da ke kudu maso yammacin Najeriyar.

10:45 Muhammadou Issoufou a lokacin da yake kada kuri'arsa cikin turmutsutsun jama'a da 'yan jarida.

10:43 Shugaban Nijar, Muhamadou Issoufou tare da masu dakinsa, Aissata da Malika sun kada kuri'a, da misalin karfe goma na safe a mazaba mai lamba 001, a Hotel de Ville. Ya bukaci 'yan kasa su yi zabe lami lafiya, kuma su zabi wanda suke so.

10:37 Shugaban hukumar zabe ta Nijar, CENI, Boube Ibrahim ya kara tabbtar da cewa hukumar za ta gudanar da zabe na gaskiya da adalci, bayan da ya kada tasa kuri'a a rumfar zabe ta Hotel de Ville dake birnin Niamey, ya shaida wa manema labarai cewa kodayake an tsara rufe rumfunan zabe da karfe 7 na yamma, amma za a kara lokaci a wurare da aka soma zabe a makare, da wuraren da karfe 7:00 ta yi amma mutane na kan layi.

10:34 Wani daga cikin wadanda ake zargin shekarunsu ba su kai ba amma kuma suna wakiltar jam'iyyun siyasa a rumfunan zabe

10:27 Wakiliyarmu ta Maradi, Tcima Illa Issoufou ta ce duk da cewa zabe yana tafiya lami lafiya amma ta ce ta ga wasu wadanda ake zargin shekarunsu ba su kai na zabe ba suna wakiltar wasu jam'iyyu a rumfunan zabe

10:17 Wakilinmu na jamhuriyar Niger, Baro Arzika wanda yanzu haka yake a mazaba ta daya da ke ofishin magajin garin Yamai ya ce mutane da dama sun kada kuri'arsu kuma ana jiran shugaban kasar da 'yan majalisarsa su kada tasu kuri'ar.

10:14 Shugaba na yanzu Muhamadou Issoufou na neman wa'adi na biyu na shekaru biyar. 'Yan takara goma sha hudu ne ke kalubantarsa, kuma cikin 'yan takarar na jam'iyyun adawa, har da tsofofin firaiyi ministoci uku.

Hakkin mallakar hoto
Hakkin mallakar hoto

10:12 Masu jefa kuri'a fiye da muliyan bakwai ne dai suka yi rijista kuma ake sa ran sun nufi rumfunan zaben domin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki, a jamhuriyar Niger.

10:03 Tun dai kimanin karfe 8:00 na safiyar nan ne aka fara kada kuri'ar

10:02 An fara kada kada kuri'ar zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki, a jamhuriyar Niger.