FA CUP: 'Ya kamata a fara bugun fanareti'

Cocin Hull city Steve Bruce Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Cocin Hull city Steve Bruce

Cocin kungiyar kwallon kafa ta Hull City Steve Bruce ya ce sun gaji da buga wasannin da ake sake fafatawa saboda yana daukar tsawon lokaci.

A ranar Asabar Hull City suka kara da Aresenal inda suka tashi 0-0 kuma yanzu zasu sake fafatawa a karo na biyar .

'Shin me ya sa ba zamu buga fenality ba? Shin me ya sa sai mun sake fafatawa da juna?

Bruce wanda kungiyarsa ce ta fi yawan maki a gasar FA ya kuma ce ba dai dai bane abin da ake yi wa magoya bayan kwallon kafa saboda sai sun nemi kudin kallon wasa