An bude taro kan shafukan zumunta a Nigeria

Tambarin Twitter Hakkin mallakar hoto
Image caption Shafukan sada zumunta sun taka muhimmiyar rawa a lokacin zaben shekarar 2015 a Nigeria.

A Najeriya, a ranar Litinin ne ake soma taron mako guda kan rawar da shafukan sada zumunta ke takawa wajen kawo sauye-sauye a duniya.

Taron, wanda ake yi a birnin Lagos, zai duba musamman yadda ake amfani da shafukan na sada zumunta wajen gudanar da harkokin siyasa, kasuwanci, harkokin watsa labarai, bunkasa ilimi da samar da ayyukan yi.

Miiyoyin mutane dai ake yin amfani da shafukan sada zumunta irin su Facebook da Twitter da Whatsapp a Najeriya.

Sai dai wasu na ganin akwai bukatar sanya idanu sosai a kan shafukan sada zumuntar, saboda yadda wasu ke amfani da su domin cin zarafi jama'a da kuma bayar da labarai karya.