Fada zai bada shaida kan lalata da yara

Fafaroma Francis Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An dade ana zargin limaman cocin da lalata kananan yara.

Fadar Fafaroma ta Vatican ta amince wa wasu 'yan kasar Australia da ake zargin cewa wasu Limaman darikar Katolika sun yi lalata da su, su kasance a birnin Rome a lokacin da wani babban Fada, mai suna Cardinal George Pell zai ba da shaida ta bidiyo, a wani bincike da ake yi.

An dai bayyana cewa George Pell na fama da rashin lafiya, saboda haka ba zai iya zuwa ya ba da shaida a gaba kwamitin binciken ba.

Wata kungiyar wadanda ke zargin an yi lalata da su na bukatar su kasance a cikin zauren Fadan zai ba da shaida.

George Pell dai babban jami'in kudi ne a fadar Vatican, kuma ana zarginsa da rufa-rufa a kan zargin da ake na lalata da wasu, lokacin da yake aiki a Australia, amma ya musanta zargin.