AU ta yaba da zaben Niger

Tambarin AU Hakkin mallakar hoto au
Image caption Wakilan kungiyar tarayyar Afurka sun yaba da zaben da aka yi a jamhuriyar Nijar.

Kungiyar Tarayyyar Afurka watau AU ta yaba da yadda 'yan siyasar Nijar da sauran al'umar kasar suka nuna halin dattako a zaben da aka gudanar a kasar ranar Lahadi da ta gabata, lamarin da kungiyar ta ce zai karfafa dimokuradiyya a kasar.

A halin yanzu dai ana ci gaba da dakon sakamakon zaben na shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki a jamhuriyar Nijar.

Hajiya Aisha Laraba Abdullahi, ita ce kwamishina mai kula da harkokin siyasa ta kungiyar tarayyar Afirkar, wadda ta shugabancin tawagar masu sa 'ido ta tarayyar Afirka a zaben na Nijar ta shaidawa BBC cewa 'yan kasar sun nuna da'a.

An kuma gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana, ba tare da an yi hatsaniya tsakanin 'yan adawa ba.

Haka kuma jami'an hukumar zabe sun nuna kwarewa ta hanyar kai kayan aiki runfunan zabe akan lokaci, duk da cewa a wasu sassan kasar an samu tsaiko na isar kayan aiki.