An zargi Ethiopia da cin zarafin 'yan adam

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A watan Nuwambar bara ne aka yi zanga-zangar a kasar Habasha.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta zargi hukumomin tsaron Habasha da kashe-kashe, da kame-kame da kuma azabtarwa domin murkeshe zanga- zangar lumana da aka fara tun watan Nuwambar bara.

Masu zanga-zanga a Oromia, wanda shi ne yanki mafi girma a Habasha, na adawa da matakin fadada babban birnin kasar Addis Ababa zuwa yanki, bisa fargabar cewa manoman wajan za su rasa gonakinsu.

Kungiyar kare hakkin bil adama, ta ce 'yan sanda na harbi a iska kan dandazon masu zanga-zanga kuma sun kama daruruwan mutane.

Gwamnatin kasar ta yi watsi da rahotan tana cewa an yi son kai a ciki.