Facebook zai yi taswirar gidajen jama`a

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption kamfanin facebook zai yi taswirar gidajen jama`a

Kamfanin Facebook ya ce zai yi amfani da manhajar Al wajen yin taswirar gidajen jama'a.

Kamfanin dai ya jarraba manhajar wajen gane gidaje da gine-gine a kasashe 20.

Ya dai amfani ne da irin bayanan da yake samu da wata manhajar da ke nazarin hotuna daga tauraron Dan'adam wajen gane gidaje da sauran gine-ginen da mutane ke yi.

A cewar kamfanin zai samar da cikakken zai yi taswirorin wuraren da ya yi amanna akwai al'uma a ciki, kuma zai ba wa jama'a damar ganin su nan da karshen wannan shekarar.

Kamfanin ya kara da cewa taswirorin za su taimaka sosai ga masu gudanar da bincike a kan tattalin arziki da walwalar jama'a, da kuma kididdigar da ta shafi irin masifu ko bala'in da kan auka wa al'uma.