Masu sayar da mota sun koka

Motoci a Nigeria. Hakkin mallakar hoto
Image caption Tashin dalar Amurka ya shafi 'yan kasuwa a Nigeria.

'Yan kasuwa da ke sayo motoci daga kasashen waje, na cewa yanayin da ake ciki ya tilasta musu dakatar da fita waje domin sayo motocin, saboda karyewa da kudin Nigeria wato Naira ya yi idan aka kwatanta da dalar Amurka.

To sai dai kuma a wani bangaren, yan kasuwar na cewa a yanzu haka wata dama ta fitar da kaya kasashen waje ta bude a tsarin nan na ba-ni-gishiri-na-ba-ka-manda.

Ambasada Mukhtar Gashash shi ne shugaban kungiyar masu sayar da motoci ta jihar Kano, ya kuma shaidawa wakilinmu a Kano Yusuf Ibrahim Yakasai cewa tashin kudin ya kai matukar da babu halin sayo motocin daga kasashen waje.

Ya yin da wasu 'yan kasuwar suka fara tunanin sauya sana'a, ta hanyar fitar da wasu abubuwa da ake yi a gida Nigeria zuwa kasashen ketare.

Misali kamar Ridi ko Zobarodo da Kanunfari ko Karo da sauransu.