Ba ni da alaka da Boko Haram- Sheriff

Sabon shugaban jam'iyyar PDP a Najeriya, Sanata Ali Modu Sheriff, ya musanta cewa yana daukar nauyin 'yan kungiyar Boko Haram.

Modu Sheriff, wanda tsohon gwamnan jihar Borno ne, ya shaida wa BBC cewa babu wata hujja da aka gabatar da ta tabbatar da zargin da ake masa:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Sanata Sheriff ya kara da cewa mutanen da ke tsoron sa, da kuma su ke ganin idan ba su yi masa sharri ba, ba za su samu damar yin suna a siyasa ba.

Ya ce shi kan sa mayakan Boko Haram sun sha yunkurin hallaka shi amma ya na tsallake-rijiya-da-baya.

Tuni dai wasu 'ya'yan jam'iyyar ta PDP a wata kungiyar da ake kira PDP Rescue group suka ce ba su ji dadin nadin da aka yi wa Ali Modu Sheriff a matsayin sabon shugaban jam'iyyar ba.

Sun kuma yi kira ga sabon shugaban da ya yi murabus.