An gina wa gimbiyar Thailand bandaki na $40,000

Image caption Gimbiya Maha Chakri Sirindhorn ta Thailand.

An gina wani bandaki da ake tunanin ya lashe kimanin dala 40,000 wanda wata gimbiyar Thailand za ta yi amfani da shi yayin wata ziyara ta kwana uku a Cambodia.

An gina bandakin ne a kusa da wani tafki inda gimbiya Maha Chakri Sirindhorn, za ta fara ziyarar, an kuma kawata shi da na'urar sanyaya daki.

Ba a bayyana wanda ya dauki nauyin gina wannan bandaki ba.

Amma za a dauke bandakin bayan ta gama ziyarar tata, za kuma a mayar da ginin ofishin wata hukuma.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da 'yan Cambodia miliyan shida ne basa samun ruwan sha mai kyau da kuma tsaftataccen muhalli.