An fara samun ruwan sha a birnin Delhi

Mazauna Delhi, babban birnin kasar Indiya sun soma samun ruwan sha a wasu yankuna bayan an fara gyara babbar madatsar ruwan da ke bai wa birnin ruwa.

Sojoji sun kwato madatsar ruwa ta Munak da ke jihar Haryana, makwabciyar birnin Delhi bayan 'yan kabilar Jat sun mamaye ta saboda zargin da suka yi cewa ana nuna musu bambanci wajen rabon mukaman gwamnati.

Ministan samar da ruwan sha na birnin Delhi, Kapil Mishra, ya ce akwai sauran rina-a-kaba dangane da rigimar da ta yi sanadiyar mamaye madatsar ruwan, yana mai yin kira ga mutane da su yi taka-tsantsan wajen yin amfani da ruwan.

An sake bude makarantun da aka rufe sakamakon mamaye madatsar ruwan.

Kimanin mutum miliyan goma sha shida ne ke zaune a birnin na Delhi, kuma suna samun akasarin ruwan shansu ne daga madatsar ruwan ta Munak.