An yi kuskuren daure dan shekara hudu

Hakkin mallakar hoto Getty

Mahukunta a Masar sun shaida wa BBC cewa an yi kuskure wajen hukuncin daurin rai-da-rai da aka yanke wa wani yaro da shekara hudu da haihuwa, wanda ake zargi da aikata kisan kai.

Wata kotun soji ce ta kama yaron da laifi a wani mummunan bore shekaru biyu da suka wuce, a wata shara'ar da aka yi a bayan idonsa.

Wannan shara'ar dai ta ja hankalin kasashen duniya, tare da sukar bangaren shara'ar Masar.

Wakiliyar BBC ta kara da cewa masu sukar lamari sun ce shari'ar yaro dan shekara hudun, mai suna ce ko da a idon shari'a a kasa irin Masar.

Lauyoyi sun ce an gabatar da takardar shaidar haihuwar yaron a lokacin shari'ar da ke nuna cewa yana da shekara biyu da haihuwa.

Sai dai Kakakin sojin kasar ya shaida wa BBC cewa an yi kuskure ne wajen yanke wa yaron hukunci, alhali wani mai suna irin nasa ne ya aikata laifin.

Yanzu dai Mahukuntan kasar sun dukufa wajen farautar mai irin sunan yaron.