Majalisar dokokin Amurka ta yi watsi da shirin rufe Guantanamo

Hakkin mallakar hoto .
Image caption 'Ya 'yan jam'iyyar Republican sun soki matakin rufe sansanin Guantanamo

'Ya 'yan jam'iyyar Republican a majalisar dokokin Amurka sun yi kakkausar suka ga shirin shugaba Obama na rufe sansanin Guantanamo dake Cuba kafin ya bar mulki.

A karkashin shirin, za'a tura wasu fursunoni zuwa kasashen waje, yayinda wasunsu kuma za a tura su wasu wuraran tsaro a Amurka.

Sai dai kuma kakakin majalisar wakilan kasar P'aul Ryan, ya ce wannan mataki ya sabawa dokokin kasar.

Shugaban jam'iyyar Republican a majalisar dattawan kasar ta Amurka Mitch McConnell, ya ce majalisar za ta dakile wannan yunkuri na shugaba Obama.

Mr Obama ya ce ci gaba da barin sansanin Gwantanamon ya sabawa manufofin Amurka, kuma ya na yin zagon kasa ga tsaron kasar.

Mutane casa'in da daya ne dai suka rage a tsare a sansanin na Gwantanamo.