Aisha Dankano ta rasu

Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Ta sha karbar lambar yabo saboda rawar da take takawa a fina-finai

Allah ya yi wa fitacciyar jarumar fina-finan Hausar nan Aisha Dankano rasuwa a ranar Talata.

Aisha wacce aka fi sani da Sima ta rasu ne bayan jinya ta makonni biyu a Kano.

Kafin rasuwarta dai ta kasance daya daga cikin fitattun jaruman da ke fitowa a matsayin uwa, kuma ta shahara sosai a dandalin Kannywood.

Tuni masoyanta da abokan aikinta suka fara nuna alhinin wannan rashi a shafukan sada zumunta da muhawara.