Abba Moro ya shiga hannun EFCC

Hakkin mallakar hoto Getty

Hukumar dake yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati ta EFCC, ta kama tsohon ministan cikin gida na Nigeria, Abba Moru.

An kama mista Moro ne bisa zarginsa da hannu a badakalar daukar ma'aikata da hukumar kula da shige da fice ta Najeriya ta yi, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 20.

Haka kuma hukumar ta EFCC ta kama tsohuwar sakataren dindin na ma'aikatar harkokin cikin gida, Anaesthesia Nwaobia da kuma wani mataimakin darakta, wanda ake zargin shi da kitsa badakalar.

A ranar Talata ne ake sa ran hukumar ta EFCC za ta gurfanar da mutanen uku a gaban wata babbar kotu da ke Abuja.