Dambazau yana ziyara a Kamaru

Image caption Abdulrahman Dambazau ya je Kamaru ne don samar da zaman lafiya a tafkin Chadi

Ministan kula da harkokin cikin gida na Najeriya Abdurahman Bello Dambazau, ya fara wata ziyarar aiki a Kamaru inda ya gana da manyan jami'an Gwamnati.

Ministan yana wannan ziyarar ce a wani mataki na neman tabbatar da tsaro a kan iyakokin kasashen da suka kafa Hukumar raya tafkin chadi.

Abdurahman Dambazau ya gana da takwaransa na Kamaru Minista Sadi Rene, inda suka tattauna a kan batun neman hanyar mayar da 'yan gudun hijirar Najeriya gida.

Kazalika sun kuma tattauna kan dangantakar da take tsakanin Kamaru da Najeriyar ta wasu fannoni daban.

Najeriya da Kamaru da Nijar da kuma Chadi suna aiki kafada da kafada ne a kokarinsu na murkushe ayyukan kungiyar Boko Haram.