Farashin Mai zai fado a duniya - Buhari

Shugabannin kasashen Nigeria da Saudiyya sun sha alwashin dawo da martabar farashin man fetur a kasuwar duniya.

Shugabannin sun gana ne a Riyadh babban birnin Saudiyya, karkashin jagorancin Sarki Salman dan Abdul'aziz.

Sun kuma amince cewa tattalin arzikinsu ya ta'allaka ne kan man fetur, kuma al'amura ba za su tafi yadda suke so ba in har farashin man fetur bai daidaita ba a kasuwar duniya.

Kasashen sun kuma tattauna kan yadda matsalar ta'addanci take zame musu barazana don haka suna bukatar yin aiki tare domin magance hakan.

"Gamayyar kasashen musulunci"
Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Fada tsakanin bangarori masu adawa da juna na kara zafi a Libya

A karon farko shugaba Buhari ya yi tsokaci kan gayyatar da Saudiyya ta yi masa na shiga cikin gamayyar kasashen musulunci don yaki da ta'addanci.

Ya ce, "Ko da bamu shiga cikin gamayyar ba to muna goyon bayanku. Ya zama dole na godewa Saudiyya don kirkiro da wannan gamayya ta yaki da ta'addanci a duniya."

Buhari ya kuma tofa albarkacin bakinsa a kan rikicin Libya, inda ya ce tsohon shugaban kasar Muammar Ghaddafi, ya horar da 'yan kasashe da dama a yankin Sahel, wanda bayan mutuwarsa suka koma kasashensu suka zama 'yan bindiga dadi.

A don haka shugabannin kasashen biyu suka yi fatan shawo kan bangarorin da ke adawa da juna a Libya don ceto duniya daga barazanar ta'addancin da rikicin zai iya jawowa.