Ana shakku kan yarjejeniyar tsagaita wuta a Syria

Syria Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rikicin Syria ya raba sama da mutane miliyan 13 da muhallinsu.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Syria, Staffan De Mistura ya bayyana yarjejeniyar dakatar da bude-wutar da aka cimma a wasu sassan Syria da cewa tana kara kwarin-gwiwa.

Amurka da Rasha ne suka ba da sanarwar cewa za a dakatar da bude-wuta a Syria, daga ranar Juma'a mai zuwa, kuma yarjejeniyar za ta fara aiki ne da tsakar dare.

An sanar da yarjejeniyar ne bayan maganar da shugaba Barak Obama ya yi da takwaransa na Rasha, Vladmir Putin ta waya.

Sai dai manyan kungiyoyin biyu, wato da kungiyar IS da kuma Al- Nusra Front ba sa cikin yarjejeniyar, lamarin da Majalisar Dinkin duniya ke cewa babban kalubale ne wajen aiwatar da yarjejeniyar a zahiri.

Mataimakin Sakataren MDD Jan Eliasson yace idan aka cimma yarjejeniyar dakatar da bude-wutar da ba ta shafi yankin da kungiyar IS da Al Nusra suka mamaye ba, to wannan babban kalubale ne da za a fuskanta wajen sa-ido.