Donald Trump ya yi nasara a Nevada

Hakkin mallakar hoto Reuters

Sakamakon farko na zaben fidda gwani tsakanin 'yan takarar shugabancin kasar Amurka karkashin inuwar jam'iyyar Republican ya nuna cewa Donald Trump, ya samu nasara a zaben da aka gudanar a jihar Nevada.

Rahotanni sun ce Donald Trump, ya samu kashi 40 cikin 100 na kuri'un da aka kada.

Wannan ne dai karo na uku da Mr Trump ke samun nasara a jere a zaben fidda gwani na jam'iyyar.

Senata Ted Cruz da Senata Marco Rubio na fafatawa don samun wanda zai zamo na biyo a tsakanin su.

Alamu sun nuna cewa Mr Trump shi ne yafi samun karbuwa tsakanin Hispaniyawa a Nevada, duk kuwa da ci gaba da nanatawar da yake yi cewa ya kamata Amurka ta gina wata katanga tsakanin kan iyakarta da Mexico don hana 'yan cirani ketarowa.