Sojoji sun dakile hari a Dikwa da ke Nigeria

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Har yanzu akwai burbushin Boko Haram a kananan hukumin jihar Borno

Rundunar sojin Najeriya ta ce a dakarun kasar da na Kamaru sun dakile wani hari da mayakan Boko Haram suka yi kokarin kai wa a sansanin 'yan gudun hijra da ke Dikwa a jihar Borno.

A cikin wata sanarwa da kakakin sojojin Najeriya, Kanar Sani Usman Kuka Sheka ya sanyawa hannu, ta ce a yayin gwabzawar tsakanin mayakan Boko Haram da Sojojin, an kashe sojan Najeriya guda da kuma wani dan kungiyar JTF.

Kazalika wasu sojoji uku da kuma 'yan gudun hijra hudu sun samu raunuka a lokacin artabun na ranar Laraba da safe.

Ko da yake sanarwar ta kuma ce sojojin hadin gwiwar sun yi nasarar kashe 'yan Boko Haram 26 tare da raunata wasu da dama.

Dakarun na musamman sun kuma samu nasarar kashe mayakan Boko Haram da dama tare da kwato makamai da kuma motoci daga hannunsu.