Iran: Ku tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro

Image caption A zabi wadanda kasashen yamma za su dinga shakkarsu, in ji Khameini

Jagoran addini na kasar Iran, Ayatollah Ali Khameni'i, ya yi kira ga jama'ar kasar da su yi amfani da zaben da za'a yi ranar Juma'a domin zaben majalisar dokokin da idan Amurka da kasashen yamma suka ce mata kule zata iya cewa cas.

Ya bayyana wadannan kalaman ne a rana ta karshe ta yakin neman zaben da Iraniyawa za su zabi majalisar masana -- wadanda ke zaben jagoran addinin kasar.

Shugaba Hassan Rouhani ya aike da sakon kar ta kwana ga dukkan masu wayoyin salula na kasar, inda yake karfafawa dukkan Iraniyawa gwiwa na su fito su kada kuri'arsu.

Iran dai na kallon Amurka da sauran kasashen yamma a matsayin 'yan adawarta.