MTN ta biya Nigeria tarar $250m

Hakkin mallakar hoto PA

Kamfanin sadarwa na MTN ya sanar da fara biyan tarar dala miliyan 250 ga hukumar sadarwa ta Nigeria, a matsayin wani bagare na tarar da aka dora masa.

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Laraba, ya ce, kamfanin ya kuma janye karar da ya shigar da gwamnatin kan dora masa tarar kusan $3.9 biliyan.

Hukumar sadarwa ta Najeriya ce dai ta dora wa MTN tarar bisa samun kamfanin da laifin kin katse layukan mutane miliyan 5.1 da ba su yi rajista ba a bara.

Sanarwa ta kara da cewa biyan kudin da kuma janye karar wani bangare ne na neman sulhu a wajen kotu.

A watan Oktobar 2015 ne dai hukumar ta sanya wa MTN tarar $5.2 billion, amma daga bisani aka rage tarar zuwa $3.9 biliyan bayan MTN ta nemi rangwame.