Tasirin shafukan sada zumunta a zaben Niger

Facebook da twitter Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shafukan sada zumunta na Facebook da twitter

Masana da masu fafutika a Jamhuriyar Niger sun ce shafukan sada zumunta na Internet sun yi matukar tasiri a harkokin siyasar kasar da ma shi kansa zaben.

Kazalika wasu 'yan siyasa sun yi amfani da shafukan na sada zumunta wajen gabatar da manufofin su ga al'ummar kasar gabannin zaben.

Shugaban kawancen kungiyoyin farar hula na KODAO, kana mai fafutika a Jamhuriyar ta Nijar, Malam Moustapha Kadi, ya shaida wa BBC cewa shafukan na sada zumunta irin su Facebook da twitter sun taka muhimmiyar rawa a zaben na Nijar.

Shafukan na sada zumunta dai sun taimaka wajen kawo sauya ra'ayoyin mutane da kuma sauya fasalin siyasa a kasashe daban-daban musamman a lokacin zabe.