'Makobtan kasashe sun sha gaban Nigeria a kasuwanci'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dogara ya ce Nigeria ta rasa tagomashin kasuwanci a yankin Afrika ta yamma

Kakakin majalisar wakilai ta Nigeria Honorabul Yakubu Dogara, ya koka cewar kasar tana asara a harkar kasuwanci ta yadda har makwantanta suke shan gabanta.

Ya ce hakan na faruwa ne sakamakon rashin kyawawan dokokin kasuwanci da kuma abubuwan more rayuwa.

A wata sanarwa da ta fito daga ofishinsa, Mista Dogara ya bukaci lauyoyin kasuwanci da su mayar da hankali kan samar da dokokin kasuwanci ingantattu da za su samar da kyakkyawan yanayi na kasuwanci a kasar.

Mista Dogara ya ce, "mun rasa tagomashin kasuwanci a yankin Afrika ta yamma. Kasuwanci ya koma sauran kasashe saboda bamu da kyawawan dokoki. Don haka dole mu sauya salo don kawo ci gaba."