Nigeria: An kafa kwamitin mayar da masu hijra yankunansu

Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Ministan tsaro na Najeriya, Mansur Dan Ali

Gwamnatin Najeriya ta kafa wani kwamiti da zai yi rangadin yankunan da aka kwato daga mayakan Boko Haram.

An dau wannan mataki ne da zummar sanin ko yankunan sun cancanci a sake tsugunar da mazaunansu da suka kaurace wa hare-haren mayakan ko a'a.

Ministan tsaro na kasar, Manjo Janar Mansur Dan'ali mai riyata ne ya kaddamar da kwamitin mai mutane 25 wadanda aka zabo su daga daukacin hukumomin tsaron kasar.

Kanal Tukur Gusau shi ne kakakin ministan tsaron ya kuma ce an dau matakin ne don su bai wa gwamnati shawara kan hanyoyin da ya kamata a bi don mayar da al'ummar yankunan garuruwansu.