Afrika ta kudu za ta janye sojoji daga Darfur

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Afrika ta Kudu sun shafe shekaru takwas a yankin Darfur

Kasar Afrika ta Kudu ta ce zata janye dakarun wanzar da zaman lafiyarta daga yankin Darfur na kasar Sudan daga watan Afrilu.

Dakarun dai sun kwashe shekaru takwas a yankin.

Sojojin na wani bangare ne da Majalisar Dinkin Duniya da Taryyar Afrika suka kafa domin kawo karshen rikicin da ake a yankin.

A bara ne mahukuntan Afrika ta Kudu suka ki bin umarnin kotun kasar na kama shugabar kasar Sudan Omar Al-Bashir, wanda kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ke nema.

Shugaba al-Bashir dai ya musanta zargin da ake masa na kisan kare dangi a yankin Darfur.