'Yan BBOG sun tuna da daliban Buni-Yadi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Makarantar gwamnatin tarayya ta Buniyadi

Kungiyar BringBackOurGirls masu fafutukar ganin an ceto 'yan matan Chibok a Nigeria, ta yi wani zama na musamman da kuma jerin gwano rike da kyandura domin tunawa da daliban makarantar Buni-Yadi da 'yan Boko Haram suka kashe.

Dalibai 29 ne aka kashe a cikin harin da aka kai shekaru biyu da suka wuce.

Zaman ya samu halartar masu fafutuka da dangin wasu daga cikin yara.

Wasu daga cikin daliban makarantar da suka halarci zaman sun ce har yanzu suna cikin alhini na abin da suka shaida ya faru ga 'yan uwansu.

Daya daga cikin shugabannin wannan kungiyar Fatima Abba Kaka, ta ce sun shirya zaman ne domin jan hankalin mahukunta ga irin halin da daliban da suka tsira daga harin suka shiga.

'Yan Boko Haram din sun kai farmakin ne a makarantar da tsakar dare, inda suka shiga dakunan kwanan daliban yayin da suke barci, suka hahharbe wasu ko suka yanka su, suka kona wasu bayan da suka cinna wa gine-gine wuta.

Karin bayani