An soke lasisin wani likita a Masar

Hakkin mallakar hoto
Image caption Yarinya mai shekaru 13 data mutu a Masar sakamakon yi mata kaciya

Wata kotu a Masar ta soke lasisin wani likita bayan da ta same shi da laifin kisa ba da gangan ba na wata yarinya mai shekaru 13 sakamakon yi ma ta kaciya.

Raslan Fadl shi ne likita na farko da aka yi wa hukunci a Masar bisa laifin yi wa mata kaciya, duk kuwa da cewa an haramta yi wa mata kaciya a kasar shekaru bakwai da suka gabata.

Masu fafutika dai sun yaba da hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari da aka yi masa, sai dai wa su rahotanni sun ce ba a daure Mr Fadl a gidan yari ba inda kuma ya ke ci gaba da aikin sa a matsayin likita.

An dai kiyasta cewa kashi casa'in cikin dari na mata a Masar an taba yi musu kaciya a kasar.