Turai na yin taro kan 'yan gudun hijira

Ministocin kungiyar Tarayyar Turai da takwarorin su na yankin Balkans suna yin taro a birnin Brussels domin dinke barakar da ke tsakanin su a kan batun 'yan gudun hijira.

Barakar dai tana barazanar wargaza kungiyar.

Kasashen Austria, Serbia da Macedonia sun dauki matakan takaita shigar 'yan gudun hijira cikin su, lamarin da ya bata ran kasar Girka, wacce ke ganin hakan zai kawo mata matsala.

Sabanin da ke tsakanin bangarorin biyu ya sake jefa tsare-tsaren Tarayyar Turai a kan 'yan gudun hijira cikin mawuyacin hali.

Fiye da 'yan gudun hijira 100,000 ne suka wuce ta kasashen yankin Balkans domin shiga Turai a wannan shekarar.

Shugaban majalisar Tarayyar Turai, Donald Tusk, ya yi gargadin cewa idan aka gaza yin sulhu tsakanin bangarorin biyu, hakan zai karfafa gwiwar Biritaniya wajen kada kuri'ar ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai a wannan shekarar.