Fifa za ta zabi sabon shugaba

Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan takara 5 ne ke neman maye gurbin tsohon shugaban FIFA Sepp Blatter

A ranar Juma'a ne hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA za ta zabi sabon shugaba a birnin Zurich na kasar Switzerland.

Ana sa ran babban taron hukumar na musamman zai kada kuri'ar amince wa da wasu sabbin sauye-sauye da ake fatan za su dawo da martabar hukumar.

'Yan takara biyar ne dai ke fatan maye gurbin tsohon shugaban FIFA Sepp Blatter, wanda aka dakatar sakamakon badakalar da ta mamaye hukumar ta zargin almundahana.

Rahotanni sun ce hukumar kwallon kafa ta Afirka, wato CAF na goyon bayan Shaikh Salman bin Ebrahim al-Khalifa dan kasar Bahrain don ya maye gurbin Sepp Blatter.