"Sojojin Kenya 180 Al-Shabab ta kashe "

Shugaban kasar Somaliya ya yi bayani a kan yawan sojojin da Kenya ta rasa a harin da kungiyar al-Shabab ta kai a kan sansanin sojin da ke el-Adde a watan da ya gabata.

A wata hira da wani gidan talbijin na Somaliya, shugaba Hassan Sheikh Mohamud ya ce sojojin Kenya 180 ne zuwa 200 suka mutu a harin.

Sai dai Kungiyar al-shabab ta ce sojojin kenya 100 ne suka rasa rayukansu, ko da yake gwamantin Kenyar har yanzu bata yi karin bayani a kan yawan sojojin da lamarin ya shafa ba.

Shugaba Hassan, yana kare kansa a kan ziyara na baya-baya nan da ya kai Kenyar.

Hakan ya biyo bayan sukar da shugaban ke sha a kafofin sada zumunta cewa ziyarar ta sa ta yi wuri, bayan harin da aka kai bakin tekun Lido da ke Mogadishu babban birnin Somaliya.

Amma Shugaba Hassan Sheikh Mohamud ya ce ziyarar domin karrama sojojin Kenyar da ya je na da muhimmanci.

Karin bayani