Oliseh ya yi murabus

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sunday Oliseh

Mai horas da 'yan wasan Super Eagles na Nigeria Sunday Oliseh ya sanar da yin murabus daga kan mukaminsa.

Sunday Oliseh ya sanar da yin murubus din ne a wani takaitaccen sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Ya ce ya dauki wannan mataki ne saboda saba ka'adoji a kwantiraginsa da kuma rashin goyon baya da yake samu tare da kin biyan hakkokinsa da mataimakansa da kuma sauran 'yan wasa.

A kwanakin baya ne hukumar kwallon kafa ta Nigeria, NFF ta gargadi Sunday Oliseh, bayan da ya sanya wani hoton biyo na mintuna takwas a ciki a shafinsana intanet, inda ya bayyana masu sukansa da cewa suna hauka.

Karin bayani